Majalisar Dinkin Duniya Ta Zargi Iran Da Wuce Gona Da Iri

Babban Sakataren MDD Antonio Guterres

Hukumar sa ido kan harkokin Nukiya ta Majalisar Dinkin Duniya, ta tabbatar cewa Iran ta zarce adadin da aka kayyade mata na inganta sinadarin Uranium, a karkashin yarjejeniyar nukiliya aka cimma da ita a shekarar 2015.

Hukumar ta sa ido kan harkokin nukiliya ta fada a jiya litinin cewa, jami’anta sun tabbatar Iran ta zarce ingantawar da aka kayyade ma ta na kashi 3.67 cikin dari, da zummar hana ta kirkiro makaman nukiliya, a madadin dage ma ta takunkumin nukiliya.

Ba ta bayyana takamaiman adadin zarce iyakar da Iran ta yi ba, to amma kafar labarai ta AP ta ruwuito mai magana da yawun Hukumar Makamin Nukiliya ta Iran na cewa Iran ta tace sinadarin uranium har zuwa kashi 4.5% zalla.

Da safiya jiya litnin dinnan ne Iran ta ce akwai yiwuwar ta ci gaba da inganta Uranium zuwa kashi 20 cikin dari.