A wani mataki na ba saban ba, shugaban hukumar kare hakkin bil adama ta Majalisar Dinkin Duniya (MDD) Michelle Bachelet ta bukaci gwamnatin Burundi ta roki gafara a kan kalaman batanci da ta yiwa mambobin hukumar bincike mai zaman kanta, lamarin da ya zubar da mutuncinsu.
WASHINGTON DC —
A ranar Laraba, jakadar Burundi a Majalisar Dinkin Duniya Albert Shingiro ya ci mutunci kuma ya yi barazanar kai karar mambobin hukumar binciken mai zaman kanta ga kotu, a wurin zaman kwamitin babban taron MDD na uku a birnin New York.
Mai Magana da yawun shugaban hukumar kare hakkin bil adama Ravina Shamdasani, ta fadawa Muryar Amurka cewa Burundi tana cikin mambobi 47 na majalisar kare hakkin bil adama ta Majalisar Dinkin Duniya, wani matsayi dake bukatar kyawawan dabi’u.
An dai kafa hukumar bincike a kan Burundi ne a cikin watan Satumban 2016. Hukumar mai mambobi uku ta fitar da rahotanni da dama a kan yawan ayyukan cin zarafin bil adama a cikin kasar, ciki har da manyan manyan laifukan take hakkin bil adama.