Majalisar Dinkin Duniya Ta Samar da Dala Miliyan 12 Domin Taimakawa Kabilar Royhingya

'Yan kabilar Royhingya suna tsrewa daga jidajensu

Kisan gillar da ake yiwa kabilar Rohingya wadanda kusan dukansu Musulmai ne a kasar Myanmar suna tserewa daga gidajensu zuwa kasar Bangladesh ya sa yanzu Majalisar Dinkin Duniya ta samar da dalar Amurka miliyan 12 domin taimaka masu

Majalisar Dinkin Duniya ta saki Dala miliyan 12, a matsayin tallafi na kai daukin gaggawa ga wadanda suke tserewa rikicin Myanmar.

A jiya Talata, karamin Sakataren janar na majalisar da ke kula da aikace-aikacen tallafawa masu bukatar gaggawa, Mark Lowcock, ya ce ana so a samar da karin abinci da ruwa da magunguna ga ‘yan gudun hijirar.

Ya kara da cewa, al’umar Bangaladesh sun taimaka matuka wajen karbar ‘yan gudun hijirar, amma kuma yanayin da sansanonin ke ciki ya kazanta, yana mai cewa idan kasashen duniya ba su kawo dauki ba, akwai yiwuwar ‘yan gudun hijirar, wadanda sun riga sun galabaita, su fuskanci mummunar matsalar rashin lafiya.

Sama da rabin ‘yan kabilar Rohingya miliyan daya ne suka tsere daga gidajensu a Myanmar tun daga watan Agusta, kuma a cewar jami’in Majalisar Dinkin Duniyar, hanyar samo bakin zaren wannan rikicin, na hannun hukomomin Myanmar.

Ya kuma kara da cewa akwai bukatar a kara kaimi wajen dakile kwararar ‘yan gudun hijirar.