Majalisar Dinkin Duniya Ta Bukaci A Yi Bincike Kan Kisan Wasu Mutane a Kamaru

Ofishin kare hakkokin bil Adama na Majalisar Dinkin Duniya ya yi kira akan a gudanar da cikakken bincike ba tare da son kai ba a kan kisan kiyashin da aka yi wa mutane 23 a wani kauye a yankin arewa maso yammacin Kamaru, inda ake magana da harshen ingilishi a ranar 14 ga watan Fabrairu.

An sami karin bayanai tun bayan aukuwar harin na tada hankali. Masu sa ido kan kare hakkokin bil adama na Majalisar Dinkin Duniya da ke yankin na Kamaru sun bada rahoton cewa yara 15 aka kashe kuma 9 daga cikin su 'yan kasa da shekaru biyar ne.

Rupert Colville

Sun kuma ce akwai mata biyu masu juna biyu cikin wadanda harin ya shafa. Daya daga cikin su ta rasu a asibiti sakamakon raunin da ta samu.

Mai magana da yawun hukumar kare hakkokin bil Adama a Majalisar Dinkin Duniya, Rupert Colville, ya ce, har yanzu ba a sami cikakken bayani akan aukuwar lamarin ba.

Amma ya shaida wa muryar Amurka cewa shaidun gani da ido sun ce mutane 40 dauke da makamai da kuma jami’an soja da na tsaro ne suka kai hari a kauyen.