Majalisar Dinkin Duniya ta baiwa Manjo Aichatou Ousmane, wata Soja daga jamhuriyar Nijar, lambar yabo akan irin rawar da ta taka a aikin Soja masamman a lokacin da aka tura ta yi aikin wazar ta zaman lafiya, a kasar Mali.
WASHINGTON, DC —
Har ila yau an tura ta zuwa yankin Diffa a jamhuriyar ta Nijar inda ‘yan kungiyar Boko Haram suka addabi jama’a, inda nanma ta taka rawar gani.
Manjo Aichatou Ousmane, ta shawarci mata masu sha’awar shiga aikin Soja dasu zo da niyyar yiwa kasar su aiki bil hakki da gaskiya domin karewa da ciyar da kasar gaba abinda tace yasa ta shiga aikin Soja.
Ta kara da cewa kowane aiki kan zo da irin nasa kalubalen, don haka ta ummarci masu sha’awar aikin dasu jajirce da zukatansu na tunkarar duk wani barazana da ka iya tukaro su akan aikin.
Domin jin sauran hiran a saurari sauti.
Your browser doesn’t support HTML5