Shi dai kamfanin man fetur na kasa ana zarginsa da hannu a cikin badakalar karkata kudin tallafin man fetur na Nera biliyan biyar da miliyan daya lokacin da gwamnati ke biyan 'yan kasuwa masu shigowa da mai daga waje.
Sanata Aliyu Sabi Abdulahi yace idan ba'a manta ba Shugaba Buhari ya karbi mulkin kasar a lokacin da tattalin arziki ke fuskantar barazanar tabarbaewa saboda cin hanci da rashawa da ya yiwa kasar katutu. Bugu da kari kuma sai farashin man fetur ya fadi a kasuwar duniya lamarin da ya kara ragewa kasar kudin shiga.
Ganin yadda kasar take, ya sa Shugaba Buhari ya dukufa kain da nain ya yaki cin hanci da rashawa da almundahana da duk wata munamuna a kasar. Sanata Abdullahi yace su ma a Majalisa dole ne su tashi su taimakawa kokarin da shugaban kasa ya keyi su kuma tabbatar kasar ba bi kundun tsarin mulki.
Yace idan aka tuna can baya shugaban Majalisar na yanzu Dr Bukola Saraki a Majalisar da ta shude ya taba tashi yayi magana akan shirin tallafin inda yace ba wani abu ba ne illa wani shiri ne na wawure dukiyar kasa a fice waje da ita. Yace wannan furucin da yayi ya jawo masa barazana ba karama ba. Amma yau bisa ga abubuwan dake faruwa gaskiya ta wankeshi.
Gwamnatin Buhari ta sha alwashin cire hannunta daga wannan shirin na bada tallafi amma tace a biya bashin da ake bin gwamnati can baya.
A shirin shigo da mai kowace lita ana sayarwa dillalan N20 amma farashin da suke sayan lita din wurin gwamnati, kudin baya shiga aljihu gwamnati. Misali kowane wata ake shigo da jirage biyar. Akan N20 kowace lita ya kamata gwamnati ta smu N2m kan kowane jirgi, wato miliyan goma ke nan kowane wata, amma babu kudin.Dalili ke nan da Majalisar Dattawa zata yi binciken kwakwaf akan lamarin.
Ga rahoton Medina Dauda da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5