Majalisar Dattawan Najeriya Tana Binciken Kamfanin NNPC

Kwamitin Man Fetur Na Majalisar Dattawa tare da shugaban Sanata Kabiru Marafa a tsakiya

Kwamiti, ta bakin shugabanta Sanata Marafa yace abubuwa ukku suke bincike a kai kamar karbar tallafi da kamfanin yayi da batun hasara da kamfani yace yayi, da batun shogowa da man gas da yadda aka rabashi sai kuma batun ajiyar mai a tankunan yan kasuwa da ake sacewa.

Sanata Kabiru Marafa shugaban kwamitin man fetur na majalisar dattawa yace akwai abubuwa ukku da zasu gudanar da bincike a kai.

Na farko basu san dalilin da ya sa aka ba kamfanin tallafi ba, bisa ga yin alakari da cewa ana bashi gangar mai 445,000 kowace rana domin ya tace ya ba 'yan Najeriya mai. Ana zaton idan ya tace ya sayar zai ci riba. Baicin wannan sai kamfanin ya dawo ya shaidawa gwamnati cewa shi ma yayi hasarar kudade shi ne aka biyashi Nera miliyan sau dubu, sau dubu kuma sau biyar wato N5.00tr

Magana ta biyu da za'a bincika akwai mai da ake kira gas wanda manyan motoci da janaretoci ke anfani dashi. Shi an cire tallafi a kanshi. Sai kwatsam kamfanin ya fara shigowa dashi lokacin da yayi tsada a kan N140 lita daya amma sai a rabawa wadanda ake so su ci ribar N150 kan kowace lita, wato su sayar N360 kowace lita. Mutun na iya cin ribar N200m ko fiye da haka. Kwamitin na son ya san yadda aka shigo dashi, lita nawa ya shigo dashi kuma su wanene ya rabawa. Shin yayi adalci a rabawan?

Magana ta ukku ita ce ta baiwa mutane ajiyar mai a tankunansu. Wasu sun gina tankuna na haya. Idan gwamnati ko wani sun shigo da mai sai su biya a ajiye a tankunan. Amma bayan gwamnati ta kawo mai ta kuma biyasu kudin ajiya sai masu tankunan su sace man su sayar. Yanzu an gano wasu mutane biyu da suka sace lita miliyan dari bayan an biyasu kudin ajiya da kudinsu ya kai Nera miliyan dubu goma sha hudu ko N14b.

Sanata Aliyu Sabi Abdullahi kakakin majalisar dattawan ya bayyana abun da suke tsammani binciken zai haifar. Yace na daya binciken zai hana yin sama da fadi da kudin jama'a. Idan aka hana sace kudin jama'a gwamnati zata yiwa mutane aiki da kudin. Gwamnati zata samu isasshen kudi ba sai tayi rance ba.

Ga rahoton Medina Dauda da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Majalisar Dattawan Najeriya Tana Binciken Kamfanin Mai NNPC - 4' 47"