Duk da korafe-korafen da aka yi ta yi akan batun kafa hukumar da za ta sa ido akan yadda ‘yan kasa ke amfani da kafafen sada zumunta na zamani, musamman ma a fanin yin kalamai irin na batanci, wanan bai hana majalisa yin aikinta ba, domin majalisar ta cigaba da yi wa dokar karatu na biyu.
Wannan dokar kariya daga batanci daga dandalin sadarwa na zamani ta sake jan hankalin ‘yan Majalisar dattawan a karo na biyu ne har aka yi tattaunawar mussamman a zauren majalisar, zaman da ya nuna galibin ‘yan majalisar suna goyon bayan wanan kudirin dokar.
Sanata Kabiru Ibrahim Gaya yana cikin ‘yan majalisar da suka nuna fa'idar wanan kudiri, inda ya jaddada cewa Kundin tsarin mulki ya baiwa kowa dama ya fadi albarkacin bakinsa amma kuma ya fadi albarkaci mai ma'ana ba zagi da karya da cin kazafi ba.
Shi kuwa Mataimakin mai tsawatarwa na majalisar dattawan, Sanata Sahabi Ya'u ya yi nuni ne cewa babu wani dalilin da zai sa gaban kowa ya fadi, saboda wannan kudurin ba zai zama doka ba sai an samu ra'ayoyin al'ummar kasa akan ta nan ba da dadewa ba.
Amma masanin dokokin kasa, Barista Mainasara Kogo Ibrahim, ya shaida cewa wanan al'amari ba sabon abu bane domin kasashe da dama suna amfani da irin wanan doka da ta ke kara karfafa zamantakewa da kuma kare hakin al'ummominsu.
Ita wannan doka dai ta sha suka kuma tana kan shan suka daga kungiyoyi daban daban, wanda daga cikinsu Sakataren Kungiyar ‘yan jaridu na Kasa Shuaibu Leman ya nuna mamakin abin da yasa ake kokarin tabbatar da wanan kuduri ya zama doka.
A halin yanzu dai an mika wanan kudurin doka ga Kwamitin kula da Harkokin shari'a domin a tsaftace shi kafin a fara sauraren ra'ayoyin al'ummar kasa akan shi.
Ga cikakken rahoton Wakiliyar Muryar Amurka a Abuja, Medina Dauda.
Your browser doesn’t support HTML5