Majalisar Dattijan Najeriya ta kafa wani kwamiti da zai duba tare da kuma gudanar da bincike akan hada hadar kudi na Bitcoin.
Yanzu haka dai Bitcoin na karbuwa tsakanin 'yan Najeriya lamarin da majalisar ta ce yana da hadari, musamman bayan da babban bankin kasar ya nisanta kansa da kudin..
Dr Dauda Muhammed Kontagora na Jami'ar Bayero ya yi karin haske akan wannan sabon kudin. Ya ce ba irin kudin da aka saba dashi ba ne. Ba takarda ba ne. Ana hada hada dashi ne ta yanar gizo tare da yin bayanan sirri ta yanar gizo da lambobi. A cewarsa a shekarar 2009 ne aka kirkiroshi. Har yanzu ba 'a san ainihin sunan wanda ya kirkiroshi ba amma ya sakaya da suna Sakamoshi Nakamoto.
Dr Kontagora ya kara da cewa matsalar kudin babu wani da yake tsakiya kamar dillali ko banki. Idan wata matsala ta faru babu wata hukuma ko gwamnati da zata taimaki mutum ya gano kudinsa.
Ahmed Usan Bala ya ce ya san batun Bitcoin amma shi bai taba hada-hada dashi ba. Ya ce ana anfani dashi ta yanar gizo sannan muggan mutane suna shiga harkar kudin.
A cewar Dr Kontagora kasashen duniya basu amince da Bitcoin ba kuma suna yiwa 'yan kasarsu gargadi su kauce masa. Har yanzu baya cikin hada hadar kudi na tattalin arziki
Ga rahoton Babanginda Jibrin
Your browser doesn’t support HTML5