'Yan jam'iyyar Republican a nan Amurka sun dade suna kokarin kawar da dokar inshorar kiwon lafiya da tsohon shugaba Obama ya kafa wajen shekaru bakwai da suka gabata.
Tun daga lokacin da aka kafa dokar 'yan Republican suka dinga adawa da ita tare da yin alkawarin cewa da zara sun samu rinjaye a majalisun kasar da shugabancin kasar zasu kawar da ita. To sun samu duka.
Shugaban kasa na yanzu dan Republican akan dokar yayi kemfen ya kuma sha alwashin kawar da ita cikin wata daya da kama madafin iko. Yau yana wata na shida da zama shugaban kasa.
Bayan kai komo da aka dinga yi sabuwar dokar ta Rupblican ta tsallake rijiya da baya a majalisar wakilan kasar. Kafin ta zama dokar da zata maye gurbin wadda Shugaba Obama ya kafa sai ta samu karbuwa a majalisar dattawa.
Ganin yadda Amurkawa suka dinga jifan 'yan majalisar wakilai a wasu jihohi ya sa 'yan majalisar dattawa yin dari dari da amincewa da dokar saboda yawancinsu zasu fuskanci zabe shekara mai zuwa.
Shugaban masu rinjaye na majalisar Mitch MCconnel ya yi ruwa ya yi tsaki wajen rubuta dokar a asirce da zummar kawota majalisa a jefa kuri'a cikin dan karamin lokaci. Hakan bai samu ba domin sanatoci biyar cikin 'yan Republican din sun ce ba zasu goyi bayan dokar ba a yadda take yanzu saboda Amurkawa fiye da miliyan 22 ne ba zasu samu inshora ba a karkashin sabuwar dokar da 'yan Republican su ke son su kafa.
Ganin irin kalubalen da zasu fuskanta ya sa dole yau shugaban masu rinjaye na majalisar Mitch MCconnel ya bada sanarwar dakatar da kada kuri'a kan dokar jibi kamar yadda suka shirya da. Yanzu ba'a sa rana ba. Dokar Obama zata cigaba da aiki ke nan sai an samu wata sabuwa.