Majalisar ta ce sanatoci ne kawai suke da alhakin cireshi idan ta kama a yi hakan.
A wata ganawa da manema labarai mataimakin shugaban masu rinjaye a majalisar Sanata Bala Ibn Na'Allah yace alhakin sauke shugabansu Sanata Bukola Saraki ya rataya ne akan 'yan majalisar.
Inji Sanatan shugabancin majalisar dattawa na majalisar ne ba na Najeriya ba ne. Idan su 'yan majalisa suka ce ya ajiye mukaminsa to akwai tasiri akan batun. Banda majalisar babu wani wanda ya isa ya matsa mashi ya ajiye mukaminsa.
Dangane da matsalar da Sanata Bukola Saraki yake ciki Sanata Bala Ibn Na'Allah yace sun tabbatar cewa babu hannun fadar shugaban kasa ciki. Yace duk sun yadda cewa dole ne su ba shugaban kasa goyon baya akan yaki da cin hanci da rashawa.
Dangane da gurfanar Sanata Bukola Saraki gaban kotu, Sanata Bala Ibn Na'Allah yace majalisar dattawa zata rungumi duk irin hukuncin da ya fito daga kotun. Yace a dokokinsu idan magana tana gaban kotu to baya hannunsu. Zasu kare duk wani hukunci da kotun ta yi.
Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari.
Your browser doesn’t support HTML5