Dokar da take neman a kafa rundunar ‘Yan sandan jiha ta sami karatun farko a gaban majalisar dattijai, sabanin abin da ya faru da dokar a baya.
Amma har yanzu tsugunne ba ta kare ba a kan dokar, saboda wasu daga cikin ‘yan majalisar ciki har da shugaban masu rinjaye Sanata Ahmed Lawal, ya ce akwai bukatar a kara nazari sosai.
Da farko kamar yadda Sanata Lawal ya ce, shi ne a gano mene ne yake hana hukumomin tsaro hana aukuwar tashe tashen hankula, rashin isassun ma’aikata ne, ko rashin kayan aiki, ko rashin horo da ya dace, ko duka uku?
Idan aka fahimci inda matsalar take, hakan zai taimaka wajen gano bakin zaren inji shi.
Senata Kabiru Garba Marafa, daga Zamfara, bai goyi bayan kafa rundunar ‘Yan sanda karkashin ikon jihohi ba.
Har ma yana kira ga ‘yan arewa su yi magana da wakilansu a majalisun tarayya da kakkausar harshe na nuna adawarsu da wannan kuduri.
Amma kakakin majalisar dattijai, Aliyu Sabi Abdullahi, ya ce an gwada a baya kuma matakin ya haifar da mai ido. Ya ce karkashin sabuwar dokar, bawai tilas bane ko wace jiha sai ta kafa rundunar ‘Yansanda.
Hakan zai dogara ne kan karfin jiha, da kuma ko tana da sha’awar yin haka.
A saurari rahoton Madina Dauda domin jin karin bayani:
Your browser doesn’t support HTML5