Majalisar Dattawan Najeriya ta sake bankado wata badakalar kudade a ma'aikatar man fetur ta kasa, inda ta gano cewa akwai wani kamfani da Gwamnatin Tarrayya ta zuba kudin jari har aka bude masa asusu da ake ajiyan Dalar Amurka.
A yanzu haka akwai kudi sama da Dalar Amurka 141 a cikin asusun.
Bincike ya nuna cewa wasu mutane su 6 ne ke sa hannu a asusun suna diban kudi ba tare da sa idanun jami'an bankin Najeriya ba.
Sukan samu damar yin hakan ne, saboda asusun ba shi da lambar tantance wanda ke da mallakin asusun, wato BVN.
Kudaden a cewar rahotanni, an ajiye su ne a bankin Keystone.
Sanato Dino Melaye, mai wakiltar Kogi ta Yamma, shi ya fara gabatar da wannan badakala a gaban majalisar.
Saurari rahoton wakiliyarmu Medina Dauda daga Abuja, domin jin sunayen mutane 6 da aka gano sunayensu akan asusun, wadanda su kadai ke iya taba su.
Your browser doesn’t support HTML5