Bayan tafka mahawara akan batun a zaman ta na jiya litinin, majalisar ta kafa kwamitin mai wakilai 7 domin gudanar da binciken.
Hon Labaran Abdul Madari wanda shine ya gabatar da kudiri kan batun ya bayyana cewa majalisa ta dauki wannan matakin ne domin a kan kundin tsarin mulki take tafiya, kuma kundin tsarin mulkin ya bukacesu, su gudanar da bincike domin tantance gaskiyar Magana, yadda zasu sanar da al’ummar da suke wakilta.
Yace yadda aka sami ci gaba a fannin hanyoyin sadarwa a Najeriya, yana iya yiwuwa a harhada hoto ya zama tamkar haka lamarin yake, sabili da haka gudanar da bincike zai taimaka wajen tantance gaskiyar lamarin.
Aikin kwamitin ya hada da samun cikakken bayani daga wadanda suka buga labarin da kuma neman kwararru a fannin tantance sahihancin labarai da hotuna da aka yayatawa a shafukan yanar gizo.
Dan majalisa Labaran Abdul Madari ya yi wannan bayanin ne a hirarsu da wakilin Sashen Hausa Mahmud Ibrahim Kwari.
Saurari cikakkar hirar:
Your browser doesn’t support HTML5