Gwamnatin kasar Nijar tare da hadin gwiwan ofishin jakadanci kasar Amurika da hukumar UNESCO sun shirya wani taron horars da ma’aikatan jarida a fadin kasar. Wannan horaswar ta biyo bayan korafi da akeyi cewar ma’aikatan jarida a kasar basu da kwarewa a harkar.
Ta bakin Mal. Yahuza Salisu Madubi wanda yake ministan sadarwar kasar Nijar ne, yayi Karin haske, yace an samar da kafafen watsa labarai masu zaman kansu a kasar, amma suna da matsaloli da dama, daya daga ciki shine shuwagabannin wadannan gidajen jaridun basu da wata kwarewa babba ta fannin gudanar da aiyukan, wannan wata hanyace da za’a basu damar fahimtar abubuwan da yakamata ace sun sani dangane da aikin jarida.
Ta bakin wata mai halartar taron Hajiya. Jamila Sule shugabar gidan radiyo Sarauniya, ta jaddada cewar lallai akwai rashin sanin makamar aiki a tare da wasu shuwagabanni da ma’aikatan, wani babbar matsalama itace ta rashin tsari, da tattala kudade da sauran abubuwa.
Your browser doesn’t support HTML5