Shahararren attajirin da ya fi kowa arziki a nahiryar Afirka, Aliko Dangote, ya ce zai yi kokarin siyan kungiyar kwallon kafa ta Arsenal a shekarar 2021.
An dade ana alakanta hamshakin mai kudin dan Najeriya da sayen kungiyar ta Gunners, wacce attajirin Ba’amurke nan Stan Kroenke ke da ita.
Dangote ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da ya yi a shirin David Rubenstein Show.
Sai ya kara da cewa, "ina kokarin kammala wani katafaren kamfani ne yanzu, bayan na gama, wataƙila a cikin shekara ta 2021 zan iya saya."
"Ba yanzu nake son siyan Arsenal ba, amma zan siya ne lokacin da na kammala dukkan wadannan ayyukan, saboda ina kokarin daukar kamfanin zuwa matakin na gaba."
Magoya bayan Arsenal sun sha suka cikin 'yan shekarun nan, yayin da kungiyar ke kokarin fafatawa a saman gasar Premier ta Ingila da kuma gaza samun damar zuwa gasar zakarun Turai.
Amma, Daraktan KSE, Josh Kroenke ya ce sun kuduri aniyar dawo da Arsenal a matakin farko.
"Burinmu na gwal ne," in ji shi, "azurfa da kofuna, ina ganin duk wani abu da ba wannan ba shirme ne." A cewar Josh.
"Akwai wasu abubuwan da ya kamata ku yi domin shimfida tushe, don cimma wadannan manufofin, kuma ina ganin mun yi hakan a cikin watanni 12 zuwa 14 da suka gabata.
"Daga cikin masu horar da mu har zuwa lokacin da muke tafiyar da kungiyar, an samu manyan sauye-sauye da suka samar da ci gaba, kuma ina matukar farin ciki da barin wadannan rukunin su ci gaba da bunkasa tare da samar da ingantaccen buri ga Arsenal a gaba."