Ma'aikatan ayyukan gaggawa a Tekun Mexico su na jera igiyoyi masu fadi na roba a duk tsawon bakin gabar Amurka a yayin da danyen man fetur mai dan karen yawa da ya malala a kan teku daga wata rijiyar mai da ta lalace a tsakiyar tekun yake gusowa ga bakin gaba. Jami'an Amurka sun ce wannan mai da ya malale yana gusawa ga gabar Jihar Louisiana da sauri fiye da yadda aka yi hasashe tun da farko.
Jiya alhamis gwamnan Jihar Louisiana, Bobby Jindal, ya ayyana dokar-ta-baci a wannan jiha dake bakin gabar tekun Mexico, a yayin da wannan mai da yayi malale yake yin barazana ga tsuntsaye da kifi da kaji da kuma namun dajin da suka dogara da bakin gabar ko tekun.
Masana yanayi sun ce yau kwana da kwanaki ke nan iska tana kadawa babu daukewa, tana turo man da ya taru a kan ruwan teku daga inda dandalin hakar mai cikin teku mai suna Horizon yayi bindiga ya nutse mako guda da ya shige. Kwararru kan abubuwan da suka shafi ruwa sun ce a bayan Jihar Louisiana, wannan mai dak yayi malale yana barazana ga wasu bangarorin jihohin Alabama, Florida, Mississippi da kuma Texas.
Tun da fari a jiya alhamisar, shugaba Barack Obama ya umurci hukumomi na tarayya da su dauki kwararan matakai na takalar wannan abinda gwamnatinsa ta kira "malalar mai dake barazana ga kasa" a cikin tekun Mexico. Shugaban ya tura wasu manyan jami'ai zuwa yankin, ya kuma bayar da umurnin yin amfani da dukkan albarkatun da ake da su wajen tare wannan mai don hana shi kaiwa ga bakin gaba, da kuma kwashe shi.