A daidai lokacin da ake kokarin hanna batun aurar da yara kanana, yanzu sai ga wani Malami makartanta, ya kokarin aurar da ‘yansa Bilikisu, ‘yar shekaru goma sha ukku, ga wani magidanci mai shekaru, hamshin da shida.
Dan uwan yarinyar yayi kira ga Gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje da Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na biyu, dasu sa baki domin hanna aiwatar da wannan auren.
Ya kara da cewa shi dai wanna mutumin da ake so a aurar wa da yariyar, yana da mata ukku, da ‘ya’ya da dama dama jikoki.
Kamar yadda jaridar Punch, ta ruwaito shi dai mahaifin wanna yarinya yana shirin aurar da yariyar ne a ranar juma’a mai zuwa da wata ‘yar uwarta da suke kusa dai dai a shekaru.
A cewar Bilkisu, bata son mutumin a duk lokacin da aka tada maganar auren sai ta fara kuka. Sarkin Kano, da Gwamnan jihar ta Kano, har yanzu babu wanda yayi wani jawabi kan batun na Bilikisu.