Mai Martaba Sarkin Kano Na Fuskantar Wasu Sabbin Zarge-zarge

A karo na biyu majalisar dokokin jihar Kano zata binciki yadda mai Martaba sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi na biyu ke tafiyar da harkokin masarautar Kano, inda har ma ta kafa wani kwamiti da zai yi bincike kan batun, kuma an ba kwamitin wa’adin mako guda ya mika rahoton sa ga zauren majalisar.

Sabon matakin majalisar na zuwa ne bayan wasu takardun korafe-korafe da wasu ‘yan Kano suka rubutawa majalisar wadanda ke bayyana rashin gamsuwa kan yadda mai Martaba Malam Muhammadu Sanusi na biyu ke gudanar da al’amuran masarautar, kamar yadda Honarable Hassan Kabiru Dashi shugaban masu rinjaye na majalisar ya bayyana.

A baya can dai, majalisar ta fara aikin bincikar sarkin na Kano dangane da zargin almubazzaranci da lalitar masarautar, amma daga bisani kotu ta dakatar da ita.

Sai dai batun shugabancin Majalisar Sarakuna ta jihar Kano ne lamari na baya-baya da ya kara tsamin dangantaka tsakanin gwamnatin Kano da sarkin na Kano.

A wata hira da Muryar Amurka ta yi da gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje a kwanakin baya, ya bayyana cewa an turawa Sarkin Kano takardar nada shi matsayin shugaban hukumar gudanar da al’amuran sarakunan jihar amma dai suna jiran amsa daga masarautar.

Rahotanni sun ce daga bisani sarkin na Kano ya rubutawa gwamnati wasikar karbar mukamin na shugabancin majalisar sarakunan Kano, amma dai babu bayanan da suka tabbatar da cewa sarkin ya kira taron majalisar sarakunan ya zuwa yanzu.

Wasu makusantan sarkin irin su Malam Ibrahim Ado Kurawa na cewa “duk kasashen da aka kirkiro masarautu babu inda aka ce sarkin da yake na asali ya zama yana karkashin wani sarki sai a Kano, inda aka ce bayan shekara biyu sarki zai sauka wani ya hau.” Ya kara da cewa wannan ya sabawa hankalin da bature yayi amfani da shi, saboda a lokacin da bature da ya zo ya bi ka’idodi.

A Larabar makon gobe ne dai kwamitin majalisar dokokin ta Kano zai mika rahoton sa game da wannan sabon zargi akan sarkin Kano, kuma rahoton ne zai tabbatar ko kuma ya kore wannan zargi.

Ga karin bayani cikin sauti.

Your browser doesn’t support HTML5

Mai Martaba Sarkin Kano Na Fuskantar Wasu Sabbin Zarge-zarge - 3'34"