An Fitar Da Sunayen ‘Yan Wasan Misiria Da Zasu Shiga Gasar Cin Kofin Afrika

Mai horar da ‘yan wasan Misra Javier Aguirre ya fitar da sunayen wasu sababbin ‘yan wasa da zasu yi wasan shiga gasar cin kofin Afrika da Nijer, da kuma wasan zumunta da Najeriya a ranakun 22 da 26 ga watan Maris, tare da manyan ‘yan wasan Misra da suka hada da Mohamed Salah na Liverpool da kuma Ahmed Hegazi mai wasan sa a West Bromwich Albion.

Mai horar da ‘yan wasan Misra dan asalin Mexico, yace yaba Salah da Hegazi da ma Ahmed Elmohamady mai wasa a Aston Villa hutu ne, saboda yawan ayyukan dake kan su a Ingila, yayin da kuma yace zai jarraba ‘yan wasan cikin gida, wadanda suka yi kokari a sansanin ‘yan wasan kafin shirye shiryen karshe a cikin watan Yuni da za a yi gasar cin kofin Afrika.

Aguirre ya kuma kira dan wasan da yafi kowa zura kwallo a raga a wasan cikin gida kuma dan wasan baya a kungiyar Zamalek, Mohamed Alaa, a karon farko da kuma Omar Gaber dukkanin su ‘yan wasan Zamalek ne, sai kuma Karim Hafiz mai wasa a kungiyar Kasimpasa.

Sai dai babu kwararren dan wasan nan da kungiyar Ahly ta saye shi a cikin watan Janairu mai suna Ramadan Sobhi da golar Misra da ya saba fara mata wasa Hussein El-Shahat, da Mohamed El-Shenawi da Ayman Ashraf sai kuma dan wasan gaba Marwan Mohsen a cikin tawagar ‘yan wasan.

A karkashin Aguirre dan asalin Mexico da aka ba shi aikin horar da ‘yan wasan Misra a wata Agustan bara, Misra ta yi nasara sau hudu a jere a wasannin shiga gasar cin kofin nahiyar Afrika.