Yarinya Ta Tashi Bom a Maiduguri

Mutane suna kalon irin barnar hare haren 'yan kungiyar Boko Haram

Harin kunar bakin wake a wata kasuwar Maiduguri ya kashe kimamin mutane goma sha shidda.

Tashin wani bam jiya Asabar a wata kasuwa dake cunkushe mutane a Maiduguri arewa maso gabashin Nigeria ya kashe akalla mutane goma sha shidda da raunana kimamin mutum ashirin.


Kafofin yada labaru sunce tana yiwuwa wata mai harin kunar bakin wake 'yar shekara goma da haihuwa ce ta tada bam din.


Wani jami'in 'yan sanda ya fadawa kamfanin dilancin labarun Reuters cewa harin kunar bakin waken, tayi damarar da nakiyoyin.

Wani sheda kuma ya fadawa kamfanin dilancin labarun Faransa cewa bam din ya tashi a lokacinda ake binciken yarinyar a kofar shiga kasuwar. Yace yana tababan idan yarinyar ta san abinda aka yi mata damarar dashi, ya kara da cewa ya tabbata daga nesa aka tada bam din da na'urar.


Nan da nan dai babu wata kungiyar data yi ikirarin cewa ita keda alhakin kai harin.


A birnin Potiskum shima a arewa maso gabashin Nigeria, wani jami'in 'yan sanda ya fadawa wani dan jarida cewa tashin wani bam da aka boye cikin wata mota daya kashe mutane biyu harin kunar bakin wake ne.


Kungiyar Boko Haram ta sha auna biranen Maiduguri da Potiskum wajen kai hare hare a baya.


Hare hare na baya bayan sun auku ne mako guda bayan da yan yakin sa kan kungiyar Boko Haram suka mamaye garin Baga a arewa maso gabashin Nigeria bayan mumunar bata kashi da sojojin Nigeria.


Jami'ai sunce tuni yan yakin sa kai suka kona yawancin unguwanin Baga da kauyukan da suke kusa. Al'amarin daya tilastawa dubban mutane arcewa zuwa au birnin Maiduguri ko kuma tsibiran tapkin Chadi.