Kama wani farar fata da aka yi cikin mayakan Boko Haram, a dajin Sambisa, na ci gaba da jan hakalin masana harkokin tsaro,
Tun bayan da Sojojin Najeriya, suka kaddamar da harin baya bayan nan na ayita ta kare daya kai ga kwato dajin Sambisa, bayan da mayakan na Boko Haram, suka tabbatar da cewa karshensu yazo, sun yi ta gudu daga dajin, yayinda jiragen yakin Najeriya, ke ruwan boma bomai daga sama, al’amarin da yasa da dama daga cikinsu aka damke su.
Duk da hukumomin Najeriya, sun ki cewa komai akan wannan batun wata majiya mai tushe a cewar wakilin muryar Amurka, Hassan Maina Kaina, tace an cafke wani farar fata a cikin mayakan Boko Haram, a dajin Sambisa.
Da yake tsokaci kanal,Aminu Isa Kontagora, yace Sojan haya an duk inda ake yaki ba wani abin mamaki bane idan har za’a biya shi Sojan haya a shirye yake yayi yaki.
Tsohon hafsa a hukumar liken asirin Sojan Najeriya, Aliko El-Rasheed Haroun, yace wannan batu na iya faruwa domin Boko Haram, nada alaka da wasu mutane, a waje.
Kawo yanzu hukumomin Najeriya, basu ce komai ba akan wannan batu na farar fata da aka kama cikin mayakan Boko Haram, a cikin dajin Sambisa.
Your browser doesn’t support HTML5