Janar Mohammad Babagana Monguno , mai ritaya, wanda kuma shi ne yake ba shugaban Najeriya shawara akan harkokin tsaro ya amsa goron gayyatar da Majalisar Dattawan kasar ta yi masa.
Sanata Muhammad Ali Ndume ya shaidawa Muryar Amurka dalilin da ya sa majalisar ta gayyaceshi. A cewarsa lokacin da majalisar ta gana da sauran jami'an tsaron kasar Janar Monguno bai samu kasancewa dasu ba. A wannan ganawar da suka yi ne suka tattauna akan matsalolin tsaro da suka addabi kasar.
A matsayinsa na mai ba shugaban kasa shawara akan harkokin tsaro dole ne majalisar ta ji daga wurinsa domin ta san abin da zata yi da zummar kawo karshen tashin hankalin dake faruwa a kasar. Musamman suna son su san matakan da zasu dauka. Ya kamata majalisa ta sani ko jami'an tsaron kasar nada isassun kayan aiki.
Samar masu da kayan aiki zai bukaci sai gwamnati ta kawo kasafin kudi na musamman domin a sayi kayan aikin. A cewarsa yanzu kasashe da dama sun amince su sayar wa kasar kayan yaki sabanin lokacin gwamnatin da ta shude saboda zargin da wasu kasashe sukayi cewa a wancan lokacin na jami'an tsaro na cin zarafin fararen hula.
Saurari karin bayani a rahoton Medina Dauda
Your browser doesn’t support HTML5