Rundanar ‘yan sanda ta kasa da kasa da kuma hukumar da ke yaki da masu yiwa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa ta EFCC, sun bayyana a yau Litinin mutumin da sunan “Mike” mai shekaru 40.
An kuma damke shi ne a wani samamen hadin gwiwa da aka kai a birnin Fatakwal a watan Yuni da ya gabata.
Hukumomin sun ce Mike ya na jagorantar kungiyoyin ‘yan damfara akalla 40 a Najeriya da Afrika ta Kudu da kuma Malaysia.
Sannan ya nada jama’ar da yakan tuntuba a kasar wadanda kan taimaka mai wajen boye kudade a China da Nahiyar Turai da Amurka, wadanda sukan bashi bayanan wasu asusu da sukan bashi damar fitar da kudade a wadannan yankuna.
Bayanai sun nuna cewa, wannan gungun ‘yan damfarar sukan gudanar da ayyukansu a kafofin sadarwa na email din kananan kamfanoni da matsakaita a akalla kasashe takwas, inda sukan nemi ma’aikatan wadannan kamfanoni da abokanan huldarsu, da su aika musu da kudade.
Akalla dala miliyan 60 wannan nau’in damfara ya tattara daga mutane daban daban, inda a wani jukon aka yaudari wani mutum ya biya har sama da dala miliyan 15.
Yanzu haka ana rike da Mike hade da wani mutum mai shekaru 38, wadanda za a tuhuma da laifukan yin kutse da da karbe kudaden mutane ta hanyar damfara.