Dokar da aka riga aka yi wa karatu na biyu a majalisar wakilai, zata iya kawo wa manyan ‘yan siyasa matsala a zabukan da za a yi nan gaba, wasu na ganin siyasa zata koma hannun 'yan boko idan dokar ta samu karbuwa.
Honarabul Mohammed Gudaji Kazaure, na daga cikin wadanda ke ganin siyasar kasar zata koma hannun ‘yan boko, kuma a ganinsa daukar wannan matakin zai kara rusa siyasar arewacin Najeriya. Gudaji ya ce shi da magoya bayansa zasu yi iyakacin kokarinsu wajen kashe dokar a lokacin da za a nemi sauraren ba'asin jama'a akanta.
Amma Honarabul Abdullahi Salame, yana ganin doka ce mai kyau domin sai mutum yana da ilimi ne zai iya kare mazabar sa a lokacin da ake mahawara a zauren majalisa.
"A saboda haka, dokar za ta kawo wa kasa ci gaba mai yawa idan har ta samu zarcewa har shugaban kasa ya sa mata hannu," a cewar Salame.
A halin yanzu, sashe na 131 na kundin tsarin mulkin Najeriya ya bada dama ga duk wanda yayi karatun sakandare ya fito takarar kujerar shugaban kasa.
Saurari Karin bayani cikin Sauti.
Your browser doesn’t support HTML5