Mahukumtan Iran Sun Cafke Wasu 'Yan Canjin Kasar Su 12

Iraniyawa sun yi cincirindo a kofar wani banki suna son sayen dalar Amurka

A wani yunkurin farfado da martabar kudin kasar mahukumtan Iran sun cafke mutane 12 'yan canji tare da rufe shagunansu yayinda 'yan kasar ke ci gaba da yin dafifi a bankuna suna neman sayen dalar Amurka wadda yanzu rial dubu 60 ke samar da dalar daya tak

Mahukuntan Iran sun kame a kalla mutane 12 dake harkan hada-hadar kasuwancin kudaden ketare a kasar. Ana zargin wadannan mutanen ne dai da kasuwancin da kudin kasar ta hanyar data sabawa doka.

Anyi wannan kamen ne domin daukar matakin ganin darajar kudin kasar bai zube ba idan aka kwatanta martaban sa da dalar Amurka.

A cikin wani rahoton da kanfanin dillacin labarai na kasar,ISNA, ya wallafa a jiya Laraba, ya ambato babban sufetan ‘yan sandan birnin Tehran, Hosseini Rahimias, na cewa an tsare wadannan ‘yan kasuwan su 12 ne a babban birnin kasar domin samunsu da kokarin yiwa kasuwancin kudin kasar zagon kasa.

Rahimi yace an kwace wasu adadin kudin da bai bayyana ko nawa ne ba daga hannu su kuma aka kulle shagunan su na hada-hadan kudaden kasashen waje har 16, duka a matsayin matakin da hukuma ke dauka akan su.

Darajar kudin Rial na kasar Iran dai, a cikin satin da ya gabata ya fadi kasa inda dalar Amurka daya aka sayar da it rial dubu 60 a kasuwar bayan fage, kamar yadda kanfanin dillacin labarai na Reuters ruwaito.

Wannan yana nufin darajar kudin ya fadi da kashi 50 daga shekara data gabata.

Yanzu haka dai ‘Yan kasar ta Iran sai sayar da Rial suke yi suna sayen dalar Amurka a cikin ‘yan makonnin nan domin nuna damuwar su akan barazanar da shugaba Donald Trump yayi na janyewa daga yarjejeniyar da aka cimmawa da kasar akan shirin nukiliyarta. Idan Shugaba Trump yayi hakan kenan zai sake sanya wa tattalin arzikin kasar takunkunmi mai tsaurin gaske a cikin watan gobe,wanda zai iya kawo nakasa ga kasar.