A cikin al'adun kabilar Abzinawa rawani nada mahimmancin gaske kuma da wuya Baabzine ya bar gidansa ba tare da daura rawani a kansa ba wanda yake kare masa rana da sanyi da iska
WASHINGTON DC —
Abdulkadir Albijir wani baazine wanda yake zaune a birnin Agadez yace ga duk baabzine babu abun da yafi rawani a duniya a wurinsa saboda shi ne kariyar darajarsa da mutuncinsa.
A al'adarsu duk wanda rawani ke kansa ana kallonsa a matsayin dattijo kuma ya kamata ya kiyaye wasu abubuwa. Ko cin abinci idan a kawai rawani a kai dole ne mutum ya hakura komi yunwa. Karya al'ada ce baabzine ya bude rawani gaban jama' ya ci abinci.
Rawnin ya kasu kashi kashi kuma kowane yana da lokacin da yakamata a yi anfani dashi.
Ga rahoton Yusuf Abdullahi da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5