Gwamnan jihar Florida Rick Scott ya gargadi mazauna gabar tekun a wani taron manema labarai da ya yi a jiya Laraba da su fita daga wurin, inda yake nuna cewa rayuwarsu da mutuwarsu na iya dogaro akan matakin da zasu dauka.
Cibiyar nazarin iskar guguwa ta kasa a Miami ta yi hasashen cewa guguwar Mathew zata kasance a a matsayi na uku a yayin da take gittawa zuwa Bahamas, amma kuma cibiyar tace jihar Florida zata huskanci ruwan sama a safiyar yau Alhamis. Al’amurra zasu dada kara tsananta a nan Florida da kuma jihar Georgia ya zuwa yammacin Juma’ar gobe.
An rawaito guguwar ta riga ta hallaka mutane goma sha daya a kasashen Haiti da jamhuriyar Dominican bayan da ta abka wa yankin a matsayin guguwa mai karfin mizani na 4, wanda ya sa ta zama guguwa mafi tsanani da ta taba abkawa kasar Haiti a cikin shekaru 52.