Mahaukaciyar Guguwar Hagibis Ta Kashe Mutane 23 a Japan

Mahaukaciyar guguwar Hagibis ta kashe mutane 23 ta kuma durkusar da harkoki a birnin Tokyo na wani dan lokaci, a yayin da mutane 16 suka bace, a cewar kamfanin yada labaran NHK yau Lahadi.

Kasar Japan ta tura dubban dakarunta da jami’an aikin gaggawa don ceto mutanen da suka makale a yankin su kuma shawo kan ruwan da ya yi ambaliya sakamakon muguwar guguwar dake tafe da ruwan sama na tarihi da aka dade ba a ga irinsa ba a kasar.

Mahaukaciyar guguwar Hagibis ta janyo ambaliyar ruwa a tsakiya da gabashin Japan kuma wutar lantarkin kusan gidaje dubu dari biyar ta katse a yankin.

An dage matakin takaita saukar jiragen sama a tashoshin jiragen Narita da Haneda amma an soke tashin jiragen sama fiye da 800 a yau, kamar yadda kuma aka dakatar da zirga zirgar jiragen kasan kamfanin Shinkansen Bullet masu gudun bala’i a wuraren da guguwar ta fi shafa.

Hukumomi sun sauke gargadin ruwan sama a yankin Kanto a kusa da birnin Tokyo, inda masu shaguna suka bude wasu kamfanonin jiragen kasa da yawa kuma suka koma aiki, amma hukumomin sun yi gargadin cewa har yanzu akwai barazanar tumbatsar rafuka a gabashin Japan kuma ruwan na ci gaba da yin barna.

Firai Ministan Japan Shinzo Abe ya kira wani zaman gaggawa ya kuma tura ministansa dake kula da harkokin shawo kan abubuwan da suka shafi bala’i zuwa wuraren da guguwar ta shafa.