Maharan sun far ma garin Chukuba ne da ke Karamar Hukumar Shiroro, inda su ka yi awon gaba da tarin shanu tare ma da kashe wani dan sanda da kuma jikkata wani, kamar yadda wani mazaunin yankin, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya yi bayani.
Shima dai Shugaban Karamar Hukumar ta Shiroro Hon., Suleiman Chukuba, wanda a yanzu haka yake cikin takun saka da kansilolinsa, ya tabbatar da kai wannan hari kamar yadda ya yi karin bayani. Ya ce shanun da ‘yan bindigar su ka sace sun kai duba guda; kuma ‘yan sandan da su ka harba har daya ya riga mu gidan gaskiya din na mobayil ne, wadanda su ka fafata da su.
A can karamar Hukumar Rafi ma an kai irin wannan hari da almurun ranar Talatan nan a garin Rigo kuma har an yi awon gaba da wasu Mutane biyar kamar yadda wani mazaunin yankin yayi karin bayani.
Da wakilin Muryar Amurka ya tuntubi kakakin Rundunar ‘Yan sandan jahar Naija, Wasiu Abiodun, akan wadannan hare hare guda biyu sai ya ce a ba shi lokaci ya yi cikakken bincike kafin ya yi bayani. Amma har lokacin hada wannan rahoton bai yi bayanin ba.
To sai dai a wani taron manema labarai a ranar Litanin din nan, Gwamnan jihar Naija, Alh. Abubkar Sani Bello, ya ce su na kokarin fatattakar miyagun daga jihar kamar yadda yayi karin bayani da cewa lallai miyagu sun yi yawa a jahar amma kuma hukuma ba za ta yi kasa a gwiwa ba, har sai ta ga bayansu.
Ga Mustapha Nasiru Batsari da cikakken rahoton:
Your browser doesn’t support HTML5