A harin maharan sun fitar da fursinonin dake daure a gidan kason. Harin ya firgita mazauna garin
Rahotanni sun ce an kashe wani fursina lokacin da aka kai harin. Malam Ibrahim Ali wanda yake zaune kusa da gidan yarin ya yiwa Muryar Amurka karin haske. Wajejen karfe goma da rabi na dare suka ji fashewar guruneti da wasu abubuwa sai suka shige gidajensu. Amma shi Malam Ibrahim ya zagaya ta wata makaranta domin ya ga abun dake faruwa. Daga gidan yarin ya ga hayaki da wuta kana masu sintiri a gidan yarin kowa yayi ta kare domin abun ya fi karfinsu.
Malam Ibrahim yace akwai mata cikin maharan kuma suna da yawa. A nasu tunanen maharan barayi ne. A gidan yarin maharan sun kwashe kowa sai mutum daya suka bari. Jami'an tsaro da sojoji dake tare hanya basu je wurin ba sai bayan da kura ta lafa.
Bayan aukuwar harin yanzu an samu kwanciyar hankali a garin na Koton Karfe. Gwamnan jihar ya je wurin har da ziyara zuwa gidan sarkin garin.
Harin baya bayan nan shi ne na biyu da za'a kai gidan yarin na Koton Karfen.
Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari.
Your browser doesn’t support HTML5