Wasu mahara da ake zanton 'yan kabilar Tarok ne gada jihar Filato sun yiwa garin Dambar dake jihar Taraba kawanya sun kuma hallaka mutane da dama.
WASHINGTON, DC —
Wasu da ake zaton yargamawa ne daga jihar Filato sun yiwa garin Dambar a jihar Taraba kawanya sun hallaka mutane da dama sun kuma chinna wa garin wuta.
Garin Dambar dake cikin karamar hukumar Ibi karo na biyu ke nan da yargamawa suka kai masa hari cikin makonni biyu lamarin da kan jawo asarar rayuka. Cikin dare suka kai hari inda suka sakawa garin wuta.
Kawo yanzu ba'a iya tantance adadin mutanen da suka yi asarar rayukansu ba ko kuma dukiyoyin da suka salwanta. Wani dan majalisar karamar hukumar Ibi mai wakiltar garin Sanusi Muhammed Sambo ya tabbatar da cewa yargamawa ne suka kai harin. Yace kwanaki sun kawo hari yanzu kuma sun sake dawowa. Yace ba zato ba tsammani suka kewaye garin. Yace wutar dake ci a garin ana iya ganinta daga nisan mil ashirin ma. Yargamawan sun shiga garin ta kowane kusurwa. Kudancin garin kuma kogin Binuwai ne ya kewayeshi.
Bayan wadanda maharan suka kashe nan take haka ma wasu da suka tsere cikin jirgin kwale-kwale sun nitse cikin kogin Binuwai a kokarin da suka yi na gujewa harin. Mata da yara da ba'a san adadinsu ba suka nitse. Duk cikin garin babu abun da ake gani sai wuta dake ci.Akwai wasu ma da suka fada cikin ruwa.
Shugaban karamar hukumar Ibi Isyaka Adamu ya tabbatar da kai harin. Yace sun sha gayawa gwamnati hare-haren da ake kaiwa yankin. Yace sun sanarda mukaddashin gwamnan jihar wanda yayi alkawarin samar da jami'an tsaro. Ya roki mutane a cigaba da yin addu'a Allah Ya kawo saukin lamarin.
Kakakin 'yansandan jihar Taraba ASP Joseph Kwaji yace akwai 'yan bindiga da suka shigo daga jihar Filato suka shiga Dambar suka kone garin kana suka kashe na kashewa kafin su koma inda suka fito. Yagargadi mutanen garin idan sun ga wanda basu sani ba to suyi maza su shaidawa hukuma.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.

Your browser doesn’t support HTML5