WASHINGTON D.C. —

Ma'aikata a kalla 100 ne su ka mutu yau Alhamis a wata mahakar ma'adinai da ke arewacin kasar Myannmar, biyo bayan gocewar laka.
An bada sanarwar aukuwar wannan bala’in ce ta kafar FACEBOOK ta ‘yan kwana-kwanan Myanmar. A garin HPAKANT ne mahakan suke hakan ma'adinan, sa’adda kasar ta goce, bayan wani ruwan sama kamar da bakin kwarya.

Wani gocewar laka da ya faru a shekarar da ta gabata a Myanmar.
Mummunar gocewar Kasa da sauran hadaruka makamantan wannan sun zama ruwan dare a yankin a ‘yan shekarun nan.
Yawancin wadanda abin ya shafa sun fito ne daga al’ummomin kabilun dake fama da talauci, wadanda ke hakan ma'adinan da manyan kamfanonin haka suka bari.