Mahajjatan Nijeriya Da Nijar Na Ta Addu'o'i

  • Ibrahim Garba

Mahajjata a Ka'abah

Wasu daga cikin Mahajjatan Nijeriya da Janhuriyar Nijar sun dukufa wurin yin addu'o'i ma kasashensu. Akasari sun fi rokon Allah ya kawo ma kasashen nasu zaman lafiya da cigaba.

Dubban mahajjatan Nijeriya da na kasar Nijar, wadanda su ka je hajjin bana na cigaba da yi wa kasashensu addu’o’i. Wakilinmu na shiyyar Adamawa Ibrahim Abdul’aziz, wanda shi ma ya sami zuwa hajjin, ya ruwaito wasu mutane na addu’o’i a Haram da Ka’aba.

Wani mai suna Abarshi Arzika daga Konni a Janhuriyar Nijar y ace ya yi addu’a ne ma ‘yan’uwa; shi ma wani dan nijar din mai suna Abu wani mai suna Abu Katoriya y ace ya yi ma Nijar addu’ar samun zaman lafiya. Shi kuma wani mai suna Umar Dan Kano, wanda ya zon daga Yola, jihar Adamawa y ace ya yi addu’ar Allah ya kawo karshen masifun da nijeriya ke fama da su.

Shi kuwa Alhaji Abdurrazak Malumfashi addu’a ya yi Allah y aba sauran Musulmi ikon zuwa Makkah. To saidai Ibrahim Abdul’aziz y ace a yayin da ake dab da rufe Filin Jirgin Saman Saudiyya da ke Jidda, akwai maniyyata aikin haji da dama daga Nijeriya da ba su samu damar zuwa ba har yanzu.

Your browser doesn’t support HTML5

09-28-2014 HAJJ - 2'15