Maniyyatan sun ce lokaci da aka basu na kawo cikon kudi yayi kadan.
Masu niyyar aikin hajji na bana a jamhuriyar Nijar, sun koka kan abunda suka kira tsawwala kudin aikin hajji, inda suka yi bayanin cewa kudin ya karu sama da jaka 162, kan abunda mahajjatan bara suka biya.
Kamar yadda maniyyatan suka ce jumlar abunda duk mai aikin hajjin bana daga kasar zai biya ya haura sefa milyan biyu.
Daga nan suka yi kira ga gwamnatin kasar ta taimaka ta rage kudin.
Amma da yake magana shugaban hukumar aikin Hajji da Umra na kasar Mal Jibirilla Bubakar, ya shawarci maniyyata da basu kammala biyan kudaden aikin hajjin bana ba,da su gaggauta yin haka, saboda bana ba kamar sauran lokuta ba kasar Saudiyya ba zata kara lokaci ba.
Your browser doesn’t support HTML5