Mahaifiyar ‘Yar’adua Ta Rasu A Katsina Da Shekaru 101

  • VOA Hausa

Hajiya Binta Dada Musa ‘Yar’adua

Allah ya yi ma Hajiya Binta Dada Musa ‘Yar’adua, mahaifiyar tsohon Shugaban Najeriya, marigayi Umaru Musa ‘Yar’adua, cikawa ranar Litinin da karfe 8 na yamma agogon Najeriya, a Asibitin Koyarwa na Katsina. Ta rasu ta na da shekaru 101 a duniya. Za a yi jana’izarta gobe Talata a Katsina din idan Allah ya kaimu.

Tuni manyan kasa da sauran jama'a su ka shiga yin ta'aziyya.