Mai magana da yawun rundunar, DSP Nafi'u Abubakar ya sheda wa kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) cewa dan nasa yana fama ne da cutar rashin lafiyar kwakwalwa.
Aliyu Umar shi ne mahaifin yaron mai shekara 12 ya alakanta daure dan nasa na shekara biyu da rashin iya siyan maganin da zai warkar da shi.
"Uban yaron ya ce ya kai shi wurin masu maganin gargajiya kuma ya sayar da wasu kadarorinsa domin ya iya biyan kudin maganin sai dai hakarsa ta kasa cimma ruwa," in ji DSP Abubakar.
Mahaifin yaron ya ce ya aikata wannan abin ne domin hana dan nasa jefe motocin mutane ko ya janyo wa kansa raunuka da za su iya sa ya rasa ransa.
A yanzu an gurfanar da mahaifin yaron a gaban wata kotu da ke Kebbi bisa laifin cin zarafi a mataki na daya.
Lamarin daure yaron dai ya auku ne a unguwar Badariya da ke Birnin Kebbi, kuma hotuna da bidiyo sun nuna yadda yaron ya rame saboda rashin ba shi abinci da kuma yadda aka ajiye shi tare da kaji.
Tun da mahaifiyar yaron ta rasu yaron ya tsinci kansa a wannan yanayin.