Biyo bayan fito da jadawalin zaben 2023 da hukumar zaben Najeriya INEC ta yi, yanzu hankali ya koma kan ‘yan takarar shugaban kasa musamman na manyan jam’iyyu.
Ba mamaki hakan ya kawar da rade-radin cewa masu ruwa da tsaki a APC na son share hanyar tsawaita mulkin shugaba Buhari ne.
Shugaban hukumar zaben ya sanar da ranar 25 ga Febrerun badi don zaben shugaban kasa da gwamnoni, bayan amincewa da dokar zabe da ta jinkirta sanarwar, kuma hakan ya kawo karshen muhawar shin dokar za ta iya aiki a tsawon shekara daya zuwa ranar zaben ne ko ranar mika mulki a 29 ga Mayun badi.
Shugabar kwamitin zabe ta majalisar wakilai Aishatu Jibir Dukku da ta ke kan gaba a ganawa da shugaba Buhari wajen rattaba hannu kan dokar ta ce shugaban na jiran lokacin mika mulki ne ga shugaba na gaba in Allah ya kai rai.
Mafi girman mukami a APC a gwamnatance da a ke tallatawa don yi wa jam’iyyar takara shi ne mataimakin shugaba Yemi Osinbajo da masu yada manufar sa su ka bude babban ofishi don fara sharar fage.
Matashi Babangida Malabu na kan gaba a masu ra’ayin Osinbajo zai iya samun karbuwa a bangarorin Najeriya.
A gefen babbar jam’iyyar adawa, su ma masu irin wannan kamfaen na karfafa cewa tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku ne zai iya tasirin dawo da PDP fadar Aso Rock.
Jagoran yada manufar mai taken “Atiku Rescue Nigeria,” Alhaji Aminu Bala ya ce ko a zaben 2019 Atiku ya tabbatar da jajircewa kan kare muradun adawa.
Masana siyasa na cewa bayan babban taron APC a watan gobe, za a samu karin manyan ‘yan siyasa da za su kafa jam’iyya ta uku mafi karfi da Sanata Rabi’u Kwankwaso ya shimfidawa tabarma.
Saurari cikakken rahoton Nasiru Adamu El Hikaya daga Abuja:
Your browser doesn’t support HTML5