Jaddada wa jama'a hadin kan dake tsakanin magoya bayan jam'iyyar Model Lumana reshen Yamai wadanda a can baya wasu bayanai na cewa suna fama da baraka bisa dalilin dake da alaka da hamayyar shugabanci, na cikin dalilin shirya gangami.
Wannan gangamin na matsayin nuna shigowar jam'iyyar cikin siyasar kasar Nijar gadan gadan ne.
Dan Majalisar Dokokin kasar ta Nijar Sumana Sanda wanda shi ne shugaban jam'iyyar a yankin Yamai yace dama can wakilan Yamai dari uku ne kawai zasu halarci gangamin sai suka yanke shawarar su hada da na sauran jihohin su halarci gangamin. Injishi, sun yi hakan ne su nuna wa Yamai da kasa gaba daya cewa jihar Yamai na hannun jam'iyyarsu da Hama Amadu.
Sai dai gangamin na zuwa ne a daidai lokacin da shugaban jam'iyyar na kasa Hama Amadu ke gudun hijira a kasar waje, matsalar da mukarrabansa ke cewa ba zata katse masu hanzarin yada akidun jam'iyyar ba.
Inji Sanda "Hama Amadu yana nan baya nan muna tare dashi. Muna son mu gaya wa mutane cewa ba wai yana kasar waje ba zai dawo ba. Nan Nijar kasarsa ce idan Allah Ya yadda zai dawo. Amma ko baya nan kokawa da zamu yi mu cimma burinmu, zamu yi."
Jam'iyyar Model Lumana dake matsayin shugabar jam'iyyun kawancen adawa ta bukaci jam'iyyun su dage wajen tabbatar da karfafa dimokradiya a kasar.
Hama Amadu dake cikin jerin mutanen da ake zargi da safarar jarirai ya fice daga kasar ne a watan Agustan shekarar 2014 bayan kwamitin gudanar wa na majalisar dokokin Nijar ya cire masa rigar kariya a shirin gurfanar dashi gaban kuliya lokacin da yake shugabancin majalisar.
Ga rahoton Souley Barma da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5