Magance Matsalar Wutar Lantarkia Nigeria

  • Aliyu Mustapha
Shugaban Nigeria yace zai ginawa kasar wata sabuwar ma’aikatar samarda wutar lantarki.

Shugaba Goodluck Jonathan na Nigeria yayi alkawarin zai gina wa kasar wata sabuwar ma’aikatar samarda wutar lantarki wadda za’a kashe tsabar kudi Dala milyan dubu ukku da rabi wajen kafa ta.

A cikin sanarwar da ya bada a ranar Talata, shugaba Jonathan yace wannan ma’aikatar da zata bada wuta mai karfin kilowatt 700, za’a kamala aikin kafa ta a cikin wa’adin shekaru hudu masu zuwa. Yace za’a sami kuddin gudanarda wannan aikin ne daga wajen gwamnatin Nigeria, kamfunna masu zaman kansu da cibiyoyin kudade da na raya kasa na duniya.

Sanarwar tace ran 24 ga watan nan na Agusta ne Mr. Jonathan zai fayyace yadda zai tinkari matsalar rashin wutar lantarki a Nigeria.

Nigeria dai ta dade tana fama da karancin wutar lantarki a sanadin matsalolin da cibiyar bada wuta ta kasar ta jima tana fama da su.