Magabatan Arewa Sun Sake Kokawa Da Halin Da Yankin Ya Fada Ciki

  • Ibrahim Garba

Duk da rashin ayyukan yi wasu matsa kan nemi na kan su

Magabatan arewacin Nijeriya sun sake nuna damuwarsu game da halin da yankin ke ciki ta fuskar tsaro da tattalin arziki.
Magabatan arewacin Nijeriya sun sake nuna damuwarsu game da halin da yankin ke ciki ta fuskar tsaro da tattalin arziki. Wani jigon Kungiyar Dattawan Arewa Furfesa Ango Abdullahi y ace abin da aka shuka ne ake girba a arewa saboda, a cewarsa, halin da ake ciki a arewa ‘yan arewar ne su ka janyo ma kansu saboda rashin ingancin shugabanci.

Shi kuwa wani fitaccen lauya mai suna Barrister Solomon Dalong ya ce babbar matsalar ita ce rashin samar ma matasa ayyukan yi da kuma kasa ilimantar da su. Ya ce sai ka ga zungureren matashi bai aikin fari balle na baki kuma bai iya sayan ko wando ma kansa. Ya ce babu fa yadda za a zauna lafiya a yanayi irin wannan. Hasalim, in ji shi, muddun aka kasa gyara al’amuran to wata rana sai Nijeriyar ma gaba dayanta ta kama da wuta.

Mambobin Kungiyar Dattawan Arewan na jawabi ne a wurin wani taron da Kungiyar Kawo Fahimta da Kuma Cigaban Juna ta jihar Adamawa mai suna “Adamawa Community Advancement Initiative ta shirya a garin Yalo.
Shi kuwa shugaban kungiyar Alhaji Bashir Ahmad cewa ya yi an shiga lokacin da ya kamata su ma kungiyoyi masu zaman kansu su bayar da gagarumar gudunmowa wurin kawo jituwa tsakanin al’ummomi daban-daban. Wakilinmu na jihar Adamawa Ibrahim Abdul'aziz ne ya turo ma na wannan rahoton.

Your browser doesn’t support HTML5

MATSALAR AREWACIN NIJERIYA