Mafita A Yajin Aikin Likitocin Najeriya

Dr. Maryamu Dija Ogebe

Likiciyar farko mace a arewacin Najeriya Dr. Maryamu Dija Ogebe ta bayyana cewa, gazawar gwamnati ke haifar da yajin aiki

A cikin hirarta da Sashen Hausa, Dr. Ogebe tace duk da yake likitici suna daukar rantsuwar kare rayukan al’umma ko ta wanne hali kafin fara aiki, suma mutane ne kamar sauran ‘yan Najeriya, sabili da haka ba za a yi masu adalci ba idan aka yi watsi da bukatunsu a kuma bukacesu su cika wannan alkawari.

Tace duk da yake bata goyon bayan yajin aikin, kamata yayi gwamnati ta rika sauke nauyin da ya taraya a wuyanta a lokacin da ya dace ba sai ta bari an shiga yajin aiki ba.

Ta bayyana cewa kimanin shekaru hamsin zuwa sittin da suka shige, ana karrama ma’aikatan jinya kwarai, ana kuma biyansu hakinsu yadda ya kamata. Duk da yake albashin bashi da tsoka, kuma babu alawus-alawus irin na yanzu, amma ana biyan ma’aikatan jinya da likitoci kan lokaci, yayinda kuma ake basu gida kusa da asibiti da mota da zarar sun kammala karatu abinda yake taimakonsu su maida hankali ga aikinsu .

Ta kuma yi kira ga hukumomi da kuma likitoci su koma teburin tattaunawa domin samun masalaha> Bisa ga cewarta, a karshe duka talakawa ne zasu wahala.

Ga hirar Dr. Maryamu Dila da Grace Alheri Abdu

Your browser doesn’t support HTML5

HIra da Dr. Maryamu Dija Ogebe Kan Yajin Aikin Likitoci-4"


Washington,DC