Mafasan Teku Sun Kai Hari Kan Wani Jirgin Ruwan Dakon Sinadari a Kusa da Gabar Nijeriya

  • Ibrahim Garba

Jirgin ruwan tankar man Italiya, irin wannda mafasan ruwan kan yi karkuwa da su

Hukumomi sun ce mafasan teku da dama dauke da bindigogi sun kai hari kan wani jirgin dakon sinadarai a kusa da gabar Nijeriya

Hukumomi sun ce mafasan teku da dama dauke da bindigogi sun kai hari kan wani jirgin dakon sinadarai a kusa da gabar Nijeriya

Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen ruwa ta kasa da kasa tace al’amarin ya faru ne jiya Alhamis a mashigar ruwan Guinea, mai nisan kilomita 80 daga birnin Lagos.

Hukumar t ace mafasan sun bude wuta kan jirgin ruwan sannan su ka yi kokarin hawa ciki, to amman bayan sun yi ta fama na awoyi sais u ka daina bin jirgin.

A wani al’amarin kuma irin wannan, jami’an kula da zirga-zirgar jiragen Girka sun ce mafasan tekun Nijeriya sun sako manyan sojojin ruwan girka biyu da su ka kama daga cikin wani jirgin dakon kayan Girka a watan jiya.

A wannan harin, wasu ‘yan bindiga dadin Nijeriya sun hau cikin jirgin su ka su ka kama jami’an biyu – wato da Kaftin din jirgin dan asalin Ukrain da kuma Injiniyan jirgin dan asalin Girka. Maharan sun kuma raunata wasu ma’aikatan jirgin su biyu.

Wannan harin kuma ya auku ne a kusa da Tashar Jirgin Ruwan Nijeriya da ke Onne, a yankin Kudancin kasar mai arzikin man fetur na Niger-Delter.