Wani rahoto yace sojoji sun tsare sarkin baka to amma kungiyoyin biyu sun karyata maganar.
Shugabannin kungiyoyin biyu sun musanta batun inda suka ce ba haka lamarin yake ba. Sabili da haka sun bukaci jama'ar Adamawa da su kwantar da hankulansu.
Mr. Philip John sakataren maharban jihar Adamawa yace sarkinsu na Adamawa suna tare dashi. Basu fuskantar wata barazana ba ko daga hukuma ko mutane. Bugu da kari suna aiki kafada da kafada da jami'an tsaro.
Shi ma shugaban 'yan kato da gora Alhaji Bako Gwani yace yanzu haka suna samun nasara. Ya bukaci hadin kan kowa da kowa a jihar domin a tabbatar an kawar da 'yan Boko Haram. A Borno da Yobe an samu hadin kan kowa da kowa.
Talakawan jihar sun nuna bacin ransu game da yadda manyan jihar ke kwashe iyalansu suna kaisu Abuja. Hatta gwamnan baya cikin jihar. Idan 'yan siyasa na yin wani abu sai su dauko jirgin sama su sauka da zarar sun gama abun da su keyi sai su bar jihar.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5