Madugun Yan Adawa A Kenya Yace Anyi Kutse A Kumputan Hukumar Zabe Aka Canza Sakamakon

Madugun yan adawar Kenya Raila Odinga yace an yi kutse mai yawan gaske da shirya rashin gakisya a kan komputocin hukumar zabe, wanda yayi sanadiyar fitar da adadin sakamakon zaben da yace na magudi ne wanda ke nuna shi a bayan shugaba Uhuru Kenyatta da rata mai yawan gaske.

Ya zuwa tsakar daren jiya zuwa yau Laraba, shafin yanar gizo na hukumar zaben Kenya ta IEBC ya nuna an kirga kashi 94 cikin dari na kuru’un da aka kada kuma shugaba Kenyata ke kan gaba da maki 54 yayin da Odinga yake da kashi 45 cikin dari a kokarin sake neman Karin wa’adi.


Shugaban hukumar zaben Wafula Chebukati yace a daidan wannan lokaci ba zai iya fada cewar an yi kutse a koputan hukumar ba, amma dai za a gudanar da bincike a kan haka.


Odinga ya karantowa manema labarai zargin da yake yi cewar masu satar bayanai sun yi nasarar kutsawa a dandalin bayanan hukumar zaben a jiya Talata yayin da ake kada kuri’a kuma sun taba sakamakon zaben shugaban kasa da ma kuru’un wasu yan adawa.