Tsohon kocin kungiyar kwallon kafa ta Manchester United Jose
Mourinho, yace kulob din Real Madrid ta gaza wajen nuna kwazo a wasan da suka buga na El-Clàsico, tsakanin ta da babbar abokiyar hamayyarta Barcelona a ranar Asabar, 2 ga watan Maris 2019 inda aka doke Real daci daya mai ban haushi.
Acikin kwanaki hudu kacal Barcelona ta samu nasara akan Real sau biyu, inda a wasan kusa da na karshe na gasar Copa del Rey Barcelona ta lallasa Madrid da kwallaye 3-0, karawa ta biyu a Santiago Bernabeau.
Mourinho, wanda ya taba horar da kungiyar ta Real Madrid a shekarun baya, ya nuna rashin jin dadi matuka, yadda wasannin tsakanin tsohuwar kungiyar tasa da Barcelona ya kaya.
Karo na farko kenan cikin shekaru 87, da Barcelona ta shige gaban Real Madrid a jimillar wasannin da suka fafata da samun nasara kan juna, inda a yanzu kididdiga ke nuna cewar, Barcelona ta samu nasara sau 96, akan Real Madrid ita kuma Real Madrid ta samu nasara kan Barcelona sau 95.
Bayan haka kuma wannan shine karo na farko cikin shekaru 15, da Real Madrid ke shan kaye a hannun Barcelona har gida sau uku a jere.
Mourinho, ya kara da cewar kungiyar ta Real tarasa kwarjini kamar yadda aka santa a baya.
Ana dai rade radin cewar Jose Mourinho, na daya daga cikin jerin masu horarwar da ake tsammanin zasu iya maye gurbin kocin Real Madrid na yanzu Santiago Solari in har kungiyar ta sallameshi.
Real Madrid dai a kakar wasan bana na Laligar kasar Spain mako na 26, tana mataki na uku ne da maki 48, banbancin maki 12 tsakanita da Barcelona, wace take matsayi na daya a Teburin, sai Sevilla a mataki na biyu da maki 53.