An gudanar da babban taron jam’iyyar Alfijir, wanda kuma ya kasance mace ce ke jagorancin jam’iyyar.
Madam Hadizatu Diallo, ta kasance mace ta farko da ta kafa jam’iyyar siyasa a jamhuriyar Nijar, domin soma gwagwarmayar siyasa a duk da sabanin aladu da na addini da ake fuskanta a kasashen nahiyar Afirka, akan shigar mata siyasar.
Hadizatu Diallo, tace “bani kadai bace amma nI ce ta farko kawo yanzu mun kai mata kimanin shida dake jagorancin siyasa a kasar Nijar”.
Kara da cewa matan da suka biyo sahun ta wajen karfa jam’iyyar siyasa karamata karfin guiwa suka yi, ta kara da cewa wannan zai taimaka masu wajen fafutuka wajen neman tsayawa zabe da kuma lashe zaben domin a cewarta mata sun fi maza yawa kuma a kowane lokaci maza ake jefawa kuri’a amma a yanzu zai tabbatar cewa duk wani shawara nan gaba da za a yi a kasar Nijar sai an nemi mata.
Shima shugaban jam’iyyar a jihar Tawa, Sulaiman Abdu Musa, yace babu banbanci tsakanin ‘ya’yan jamhuriyar Nijar ila dai sabani na akida tunda a cewarsa abu daya kowa ke yaki dashi a cikin kasar kuma wannan shine rashin kwanciyar hankali.
Your browser doesn’t support HTML5