Kanar Abdulaziz yace a jiya Laraba 22 ga watan Fabrairu wasu 'yanbindiga suka kaiwa sojojin Nijar hari a wajen da suke sintiri a wani kauye mai tazarar kilimita 16 daga Tilwa a jihar Walam dake yankin Tillabery.
Sanarwar ta cigaba da cewa sojoji biyu ne suka rasu kana wasu 18 suka ji rauni yayinda kuma wasu 14 suka yi batan dabo a sakamakon harin.
Tuni aka bi sawun maharan domin cafkosu, inji Kanar Abdulaziz. To saidai bai bayyana ko an samu hasarar wasu farar hula da dukiyoyi ba.
Gwamnatin Nijar ta isar da ta'aziyarta ga iyalan sojojin da suka rasa rayukansu a sakamakon harin sannan ta kara da jinjinawa sojojin Nijar da yadda suke sadakar da rayukansu domin kare kasar Nijar da jama'arta daga hare-haren ta'adanci.
Yankin Tillabery mai makawaftaka da kasar Mali na fama da hare-haren ta'adanci da kuma aika aikar barayin shanu kamar yadda abun yake akan iyakar Nijar da Burkina Faso ko Mali da Burkina Faso lamarin da ya sa kasashen ukku suka fara tunanen kafa rundunar soji ta hadin gwuiwa domin yakar ta'adanci.
Ga rahoton Souley Barma da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5