Ma'aikatan W.H.O Sun Tallafawa 'Yan Gudun Hijira Da Kayayyaki

Tallafi daga ma'aikatan WHO

Ma'aikatan hukumar lafiya ta duniya watau W.H.O sun taimakawa 'yan gudun hijira dake sansanin 'yan gudun hijira na Bocolis dake garin Maiduguri.

Ganin irin matsanancin hali rayuwa da ‘yan gudun hijira ke ciki a jihar Borno, ma’aikatan samar da kiwon lafiya na Majalisar dinkin duniya watau W.H.O, sukayi karo karo cikin albashinsu domin bada tasu gudummuwa wajan taimakawa ‘yan gudun hijira masammam wadanda ke cikin garin Maiduguri.

Wannan dai shine karo na farko da aka samu irin wannan tallafi daga kungiyoyi masu zaman kansu da suka cire wani abu cikin albashinsu wajan tallafawa ‘yan gudun hijira wadanda mafiya yawansu matane wadanda suka rasa mazajensu kuma aka barsu da marayu.

Ma’aikatan na W.H.O, sun kai tallafin ne ga sansanin ‘yan gudun hijira dake Bocolis, inda ake tattare da ‘yan gudun hijira kusan dubu hudu a wannan sansanin kadai da suka fito daga kananan hukumomin Abadam da Mobar, sun dai raba kayayyaki abinci ne da kayan kwanciya da kuma kayayyaki bukatun yau da kullum.

Daya daga cikin wadanda suka amfana da tallafin Yagana Umar, tyace sun yaba da taimakon amma ta koka kan rashin ingantatcen ilimi ga ‘ya’yansu a sansanin.

Malam Ibrahim Abdullahi,shugaban ma’aikatar W.H.O, yace kasancewarsu suna gudanar da aikace aikace a sansanonin ‘yan gudun hijira kuma da ganin irin wahalar da suke fuskanta yasa ma’aikatan suka hada kai domin bada tasu gudummawar wajan tallafawa ‘yan gudun hijirar.

Your browser doesn’t support HTML5

Ma'aikatan W.H.O Sun Tallafawa 'Yan Gudun Hijira Da Kayayyaki - 3'16"