Wani daga cikin ma’aikatan da ya nemi a sakaya sunansa saboda dalilan tsaro, ya bayyanawa wakilinmu Ibrahim Abdulaziz yadda gwamnatocin jihar suna bi sahun juna wajen danne musu albashin nasu.
Ya nuna cewa, gwamnan jihar da ta shude ta Murtala Nyako ce ta dauke su aiki, sai dai bai wuce wata day aba a lokacin bayan daukarsu sai aka sauke shi daga gwamnan jihar.
Daga nan kuma sai gwamantin Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri ta zo, ita kuma bata musu komai akai ba. Hasali ma mutumin yace, maimakon ya magance musu matsalar sai ma ya dauki nasa ma’aikatan na daban.
Bayan saukar Fintiri sai Gwamnatin Bala James ta hau shima ba abinda ya faru na warakar matsala. To yanzu kuma ga gwamanatin Bindo Jibrilla da ta hau mulki, itama ta ki musu komai akai.
To don jin kan wannan lamari ta bangaren gwamnatin jihar mai ci a yanzu, wakilin namu ya tuntubi Kwamishinan yada labaran jihar Malam Ahmad Sajo. Inda yace suna kan tantance adadin wadanda aka dauka ne.
Sakamakon kunbiya-kunbiyar da aka samu tsakanin lamari na saka sunayen wasu ma da ba a daukesu aikin ba don kawai cin albashi a matsayin ma’aikatan bogi. To amma a karshe Kwamishinan ya tabbatar da cewa da sun tantance sahihan ma’aikatan, to za su biya su hakkokinsu. Ga cikakken rahoton a kasa.
Your browser doesn’t support HTML5